Isa ga babban shafi

Sama da mutane dubu 100 sun fice daga Rafah na Gaza bayan umarnin Isra'ila

Isra’ila ta sanar da kwashe mutane sama da dubu 100 kawo yanzu a yankin Rafah na Gaza, bayan bukatar hakan da yammacin jiya a shirye-shiryen da take yi na kadddamar da yaki a yankin mafi yawan jama’a yanzu haka a Gaza.

People flee the eastern parts of Rafah after the Israeli military began evacuating Palestinian civilians ahead of a threatened assault on the southern Gazan city, amid the ongoing conflict between Isr
Sama da mutane dubu 100 sun fice daga Rafah yanzu haka REUTERS - Hatem Khaled
Talla

Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da zaman tattaunawar tsagaita wuta ta kasar Masar ta sami tsaiko, bayan tashin mummunan rikici tsakanin dakarun Hamas da sojojin Isra’ila da yayi sanadin mutuwar mutane 22 cikin daren jiya.

Kasar na zargin Rafah da zama matattarar mayakan Hamas a yanzu haka, don haka ta sha alwashin yin duk mai yiwuwa don fatattakar su.

Bayanai sun ce dakarun Isra’ila na ajiye mutane a wajen da ke da nisan  kilomita 20 daga garin na Rafah, lamarin da ke kara jefa fargaba a zukatan jama’ar yankin.

Wannan ta sa kasar bayar da bayanin cewa kwashe mutanen na wucin gadi ne wato, zasu koma da zarar ta gama luguden wutar da take shirin yi.

To sai dai da yake bayani guda daga cikin manyan jami’an kungiyar Hamas Sami Abu Zuhri ya ce wannan aiki ne mai matukar hadari, kuma a shirye suke su mayar da martani.

Rahotanni daga yankin na cewa jama’a sun fara amfani da jakuna don kwashe kaya da kananan yara, yayin da wasu ke takawa a kasa.

Majalisar dinkin duniya ta zargi Isra’ila kai tsaye da hana isar da kayan agaji ga Palasdinawa na Gaza lamarin da ya haifar da yunwa mai matukar tsanani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.