Isa ga babban shafi
Turai

Faransa da Jamus sun dau mataki kan bashin Girka

Bayan da suka shirya yadda za a baiwa bankunan kasar Girka Karin kudi don su farafado, shugabannin kasashen Faransa da Jamus sun lashi takobin kawo karshen matsalar bashin da ke addabar kasashen yankin daga nan zuwa laraba mai zuwa. Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Markel, ta ce rawar da kasashen nasu za su taka kan lamarin na da muhimmanci.Ba a sami wani bayani kan tattaunawar da shugabar asusun lamani na duniya IMF Christne Lagarde, ta yi da shugaban hukumar hadin kan nahiyar Turai Herman Van Rompuy da babbabn jami’in hukumar Jose Manuel Borroso ba.Amma Shugaban Faransa, Nickolas Sarkozy yace tarukan na da muhimmanci wajen shawo kan matsalar ta bashi a nahiyar. 

Shugaban Faransa Nicolás Sarkozy da Shugabar Gwmantin Jamus Angela Merkel
Shugaban Faransa Nicolás Sarkozy da Shugabar Gwmantin Jamus Angela Merkel REUTERS
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.