Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun kashe mutane sama da 100 a kauyen Mushu da ke Filato

Rundunar sojin Najeriya ta ce an kashe mutane sama da 100 a wani farmaki da gungun mahara suka kai a kauyen Mushu da ke jihar Filato.

Wani yanki a jihar Filato da ke Najeriya
Wani yanki a jihar Filato da ke Najeriya GIANLUIGI GUERCIA / AFP
Talla

Mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya ta musamman wato ‘Operation Safe Heaven’ a jihar ta Filato, Kaftin Oya James ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, an kai hari kan kauyen Mushu da tsakar daren ranar Asabar.

Wani mazaunin kauyen kuma mai suna Markus Amorudu, ya ce gungun ‘yan bindigar sun yi musu bazata kasancewar sun afka musu ne yayin da suke tsaka da barci, inda da duk da cewar da dama daga cikinsu sun boye, sai da aka yi awon gaba da wasu, baya ga wadanda suka jikkata.

Har yanzu dai ba a gano dalilin kai farmakin ba, zalika ba a kuma tantance ‘yan ta’addan da suka tafka ta’asar ba, sai dai tuni aka aike da tarin jami’an tsaro zuwa kauyen na Mushu da ke karamar hukumar Bokkos, domin tabatar da   doka da oda.

Al’ummar jihar Filato dai sun shafe shekaru da dama suna fama da tashe-tashen hankula da suka hada da rikicin kabilanci da kuma hare-haren ‘yan bindiga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.