Isa ga babban shafi

'Yan bindigar Najeriya sun nemi diyyar triliyan 40 fiye da kasafin kudin kasar

Yan bindigar da suka sace wasu fadawan sarki a kauyen Gonin Gora na karamar hukumar Chikun da ke jihar Kaduna ta arewacin Najeriya sun bukaci a biya su fansar naira triliyan 40 da motoci kirar Hilux guda 11 da baburan hawa guda 150 kafin su saki mutanen.

'Yan bindiga sun addabi Najeriya
'Yan bindiga sun addabi Najeriya © dailypost
Talla

Ranar 28 ga watan Fabrairun da ya gabata ne ‘yan bidiga suka kustsa kai kauyen tare da yin awon gaba da mutanen.

A yammacin jiya litinin ne ‘yan bindigar suka fitar da wannan bukata da ta bar ‘yan Najeriya cike da mamaki, kasancewar kudaden da ‘yan bindigar ke bukata ya kusan ninka adadin kasafin kudin kasar baki daya.

Bukatar wadannan kudade na ban mamaki a matsayin kudin fansa na zuwa ne kwanaki hudu bayan da ‘yan bindiga suka kwashe daliban firamare da sakandaren Kuriga ta jihar Kaduna kusan 300.

Satar mutane domin neman kudin fansa na ci gaba da fadada a Najeriya, inda ‘yan bindigar suka mayar da hankali kan dibar dalibai da kuma mata.

Bayanai sun ce cikin mako guda ‘yan bindiga sun sace mata da dalibai sama da 500 a arewacin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.