Isa ga babban shafi

‘Yan Najeriya da dama na da hannu wajen satar ‘danyan mai - NNPC

Shugaban kamfanin man fetur na NNPC a Najeriya, Malam Mele Kolo Kyari, yace mutane da dama a cikin kasar na da hannu dumu dumu wajen satar danyen man da kamfanin ke hakowa abinda ke hana kasar samun kudaden da ya dace ta samu.

Wasu mutane yayin ratsa wa ta cikin wata haramtacciyar matatar danyen man fetur da aka kaurace wa amfani da ita a wani yanki na jihar Bayelsa. 18 ga Mayu, 2013.
Wasu mutane yayin ratsa wa ta cikin wata haramtacciyar matatar danyen man fetur da aka kaurace wa amfani da ita a wani yanki na jihar Bayelsa. 18 ga Mayu, 2013. AP - Sunday Alamba
Talla

Kyari wanda ke bayani ga kwamitin Majalisar Dokokin kasar na musamman dake gudanar da bincike akan matsalar satar man, yace a cikin shekara guda kawai sun gano yadda aka fasa bututun har sau 9,000 domin satar danyan man.

Shugaban kamfanin yace daga shekarar 2022 zuwa wannan lokaci, kamfanin NNPC ya yi nasarar lalata haramtattun matatun man da ake amfani da su wajen tace man satar ana sayarwa jama'a.

Kyari ya kuma bayyana cewar a tsakanin wannan lokaci sun gano wurare 5,570 da aka dasa kan famfo daga bututun mansu ana sata, yayin da suka yi nasarar cire 4,876 daga cikinsu.

Shugaban kamfanin ya ce wasu daga cikin irin ta'addancin da suke gani ake yi wa bututun man hankali ba zai iya dauka ba, yayin da su kuma basu da karfin da za su iya dakile shi, ganin yadda ake musu zagon kasa wajen sake fasa bututun da zarar sun katse na satar.

Kyari yace wasu daga cikin wadannan wuraren da ake satar man na kusa da garuruwa, wasu kuma ba su wuce mita 100 daga cibiyar karamar hukuma ba, amma kuma kowa sai ya kauda kansa, abinda ke nuna cewar mutane da dama na da hannu a cikin satar man.

Shugaban kamfanin NNPCn ya ce Najeriya na da hurumin samar da ganga miliyan 2 na danyan man kowacce rana, amma satar man na musu zagon kasa, abinda ya sa a yanzu ganga miliyan guda da dubu 600 kawai suke iya samar wa kamar yadda aka yi hasashe a cikin kasafin kudin bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.