Isa ga babban shafi

Najeriya: An kama wani kwarto da ya yi shigan mata a jami’ar Kano

Jami’an tsaron Civil Defence a jihar Kano sun sanar da cafke wani mutum mai suna Muhammad Munzali, bayan da ya badda kama ya yi shigan mata ya kutsa dakin kwanan dalibai mata a jami’a mai zaman kanta ta Skyline da ke birnin Kano a arewacin Najeriya.

Dakin kwanan dalibai mata na jami'ar Ile Ife da ke jihar Osun a Najeriya. 22/02/2007
Dakin kwanan dalibai mata na jami'ar Ile Ife da ke jihar Osun a Najeriya. 22/02/2007 AP - GEORGE OSODI
Talla

Jami’in hulda da jama’a na hukumar NSCDC, Ibrahim Abdullahi, ya tabbatar da kama wanda ake zargin, a wannan Juma’a.

Jami’an ya ce gardin ya yi kokarin kutsawa bangaren kwanan dalibai matan jami’an ne da misalin karfe 10 na daren Laraba, inda masu tsaron bangaren suka cafke shi.

"An ce wanda ake zargin ya yi shigar burtu kuma ya sa kayan mata sannan kuma an same shi da laya a jikinsa,"

A cewar Abdullahi, ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin kutsawa bangaren dakin kwanan dalibai na jami’a mai zaman kansa.

A shekarar 2021, an samu wani mutum da ba a san ko wanene ba, wanda ya yi shigar burtu ya kutsa cikin dakin kwanan dalibai na jami’ar ilimi ta Ignatius Ajuru da ke Fatakwal a jihar Ribas, inda ya shiga hannun dalibai da suka tube shi tsindir.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.