Isa ga babban shafi

Akwai yuwuwar fara shigo da doya Najeriya daga China idan ba a kara azama ba

Gwamnatin Najeriya ta ce nan gaba kadan ‘yan kasar zasu fara shigar da doya daga China duk kuwa da cewa kasar ke da kaso 67 na yawan doyar da ake fitarwa a duniya.

Wata kasuwar Doya da ke garin Ibadan a yankin Kudancin Najeriya
Wata kasuwar Doya da ke garin Ibadan a yankin Kudancin Najeriya REUTERS - TEMILADE ADELAJA
Talla

Babban sakataren ma’aikatar noma da raya karkara Ernest Umakihe ne ya bayyana hakan yayin da yake bayani a wajen taron masu ruwa da tsaki kan harkokin noma da ya gudana a birnin tarayyar kasar, Abuja.

Ya ce a yanayin yadda China ta shiga kasuwar cinikayyar doya a duniya da karfin ta, da kuma irin tasirin da take da shi a kasuwar duniya za ta iya cika kasuwar Najeriya da doyar da take samarwa.

Ya ce wannan shine lokacin da ya kamata a ce ‘yan Najeriya su mayar da hankali wajen noman doya, la’akari da farin jinin da take da shi a kasashen duniya da kuma kudaden da ake samu.

Ya koka a kan  yadda wannan lamari ka iya haddasa rashin aikin yi ga dimbim matasan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.