Isa ga babban shafi

Kotu ta yankewa dan China hukuncin kisa bayan kashe budurwarsa a Kano

Babbar kotun Jahar Kano da ke tarayyar Najeriya, ta yankewa dan kasar China Frank Quandong Geng, da ake tuhuma da laifin kashe budurwarsa Ummulkusum Sani Buhari (Ummita) hukuncin kisa.

Dan China tare da budurwarsa Ummita da ya yiwa kisan gilla a unguwar Janbulo da ke jihar Kano a arewacin Najeriya.
Dan China tare da budurwarsa Ummita da ya yiwa kisan gilla a unguwar Janbulo da ke jihar Kano a arewacin Najeriya. © RFI Hausa
Talla

A hukuncin da alkalin kotun mai shari’a Sanusi Ado Ma’aji ya yanke a ranar Talatar nan, ya ce kotun ta sami wanda ake zargin Geng da laifin kashe Ummita ta hanyar daba mata wuka a watan Satumbar shekarar 2022, a lokacin da wata takaddama ta shiga tsakaninsu.

A lokacin sauraron shari’ar, Geng ya ce Ummita ta yaudareshi a soyayyar da suka yi, duk da makudan kudaden daya kashe mata bisa alkawarin auren da ke tsakaninsu.

Geng ya ce a lokacin da suka tsaida maganar aure a tsakaninsu, ya bata naira miliyan daya da rabi don siyan kayan fitan biki, da kuma naira dubu dari 7 na liki a ranar bikin.

Hakan a lokacin da ya ziyarci ‘yan uwanta a Sokoto, ya kashe naira dubu dari 7, bayan nan yana daukarta zuwa wuraren shakatawa da kuma yi mata wasu hidundumu.

Mutumin dan asalin kasar China ya ce matsalarsu ta samo asali ne a ranar 13 ga watan Satumbar shekarar 2022, bayan da Ummita ta bukaci ya bada kudi don ci gaba da aikin gidanta na Abuja da ya ke yi mata, sai dai a lokacin bayada kudi, lamarin da ya sanya ta ke ganin kamar ya talauce ne kuma daga nan bata sake daukar kiransa ba.

Frank Quandong Geng, ya ce ba wai da gangan ya kashe Ummita ba, hakan ya faru ne a lokacin da yake kokarin kare kansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.