Isa ga babban shafi

Gwamnan Kano ya yi wa maniyyata hajjin bana ragin kudi

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta rage wa dukkanin maniyyatan hajjin bana naira dubu 500 kan kowacce kujera biyo bayan karin da Hukumar Alhazan Najeriya ta yi har kusan naira miliyan 2. 

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf © Abba Kabir Yusuf
Talla

Gwamnan ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook a wannan Larabar a daidai lokacin da ake ci gaba da cece-kuce kan yadda aka tsauwala farashin kujerar hajjin a bana.

Sakamakon karin kudi har kimanin Naira miliyan daya da dubu dari tara (1,900,000) da Hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya ta yi akan kowacce kujerar aikin Hajji, ina farin cikin sanar da dukkanin maniyyatan jihar Kano cewar Gwamnatin Kano ta musu ragin Naira dubu dari biyar (500,000) akan kowacce kujera. Inji Gwamnan Kano.

Sanarwar ta kara da cewa " Wannan ragi da muka samar a yanzu haka na nufin duk wani maniyyaci da ya biya naira miliyan hudu da dubu dari bakwai (4,700,000) kudin babbar kujera da wadanda suka biya naira miliyan hudu da dubu dari biyar (4,5000,000) kudin karamar kujera za sucika Naira miliyan daya da dubu dari hudu (1,400,000) ne kacal maimakon Naira miliyan daya da dubu dari tara (1,900,000).

Sai dai tuni 'yan Najeriya  musamman mazauna yankin arewacin kasar suka fara tsokaci kan matakin na gwamnan Kano, inda wasu ke yin san-barka, yayin da wasu ke cewa, bai kamata gwamnan ya dauki nauyin biya wa duk wani maniyyaci naira dubu 500 ba, ganin irin halin matsin rayuwa da ake fama da shi a kasar.

Daya daga cikin masu bibiyar shafin RFI Hausa, Real Taheer Shehu, ya bayyana ra'ayinsa da cewa, 

Wannan ai ba shi mutane suke bukata ba duk wanda ya biya Makka yanzu ba talaka ba ne kuma ba ya bukatar tallafi, ya kamata a yi wa talaka aiki.

Sai dai Nura Isyaku na da ra'ayin da ya banbanta da na Shehu, domin kuwa jinjina wa gwamnan ya yi, yana mai cewa,

A karon farko ka yi aikin da al'umma za su amfana a zamanka na gwamna a jihar Kano

Tuni wasu daga cikin maniyyatan na Najeriya suka bayyana cewa, za su bukaci Hukumar Alhazan Najeriya da ta maido musu da kudinsu da suka biya saboda karin da aka yi musu na kusan naira miliyan 2 a lokaci guda, abin da suka ce ya fi karfinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.