Isa ga babban shafi

Najeriya na fargabar ƙarancin ɗanyen mai ko da an gyara matatun man kasar

Ƙaramin minista a ma’aikatar albarkatun man fetur a Najeriya, Heineken Lokpobiri, ya jaddada fargabar da ya ke da ita   ta cewa sabuwar matatar man fetr ta Dangote da aka ƙaddamar  kwanan nan, da matatun Port Harcourt, Warri da Kaduna, waɗanda ake sa ran kammala gyarar su ba da jimawa ba  za su fuskanci matsalar ɗanyen man da za su rika tacewa idan har ba a ƙara yawan ɗanyen man da ake haƙowa a ƙasar ba.

Wani ɓngare na matatar ɗanyen mai a garin Port Harcourt a Najeriya.
Wani ɓngare na matatar ɗanyen mai a garin Port Harcourt a Najeriya. AFP - PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Lokpobiri ya bayyana wannan fargabar a karo na 3 kenan a cikin watanni 4, a yayin wani taro na ɓangaren man da ya gudana a ranar Talata a babban birnin tarayyar ƙasar, Abuja.

Makasudin wannan taro dai kamar yadda takensa ya bayyana, shine: Ƙarfafa haɗin gwiwa don kawo ci gaba a ɓangaren mai, kuma ministan ya ce burin taron shine ɓullo da hanyoyin cimma muradan da aka sanya a gaba na ƙara yawan man da ake samarwa, don samun ƙarin kuɗaɗen shiga.

Ministan ya ce ɗaya daga cikin ƙalubalen da ke sanya masa fargaba shine, a gama gyarar dukkannin matatun mai na ƙasar,  ga kuma na Dangote da BUA, kuma a ce babu ɗanyenn man da za a riƙa tacewa.

A watan Nuwamban shekarar 2023 ne Lokpobiri ya fara bayyana wannan fargabar a yayin wani taro makamancin wannan, lokacin da wani ɗan jarida ya yi masa tambaya a game da ɗanyen man da za a riƙa tacewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.