Isa ga babban shafi

Najeriya na jana'izar sojojinta 17 da aka yi wa kisan gilla a jihar Delta

Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta kammala dukkanin tsare-tsaren gudanar da jana’izar jami’anta 17, da aka yi wa kisan gilla a yankin Okuama da ke Jihar Delta.

Shugaban Najeriya na daga cikin wadanda za su halarci jana'izar sojojin 17 a Abuja.
Shugaban Najeriya na daga cikin wadanda za su halarci jana'izar sojojin 17 a Abuja. © MNJTF
Talla

A wata sanarwar da rundunar ta fitar a shafinta na X, ta ce a yau ne za a gudanar da jana’izar a babbar makabartar kasar da ke Abuja, da misalin karfe 3 na rana.

Sanarwar ta ce shugaba Bola Ahmed Tinubu na daga cikin wadanda za su halarci jana’izar.

Idan dai ba a manta ba, a tsakiyar wannan watan ne wasu ‘yan ta’adda suka yi wa sojojin da ke aiki a karkashin bataliya ta 181 kisan gilla, bayan da suka je daidaita wani rikici da aka samu tsakanin al’umomin Okuama da Okoloba a Jahar Delta, lamarin da tuni shugaban kasar ya bada umarnin gano masu hannu wajen aikata laifin.

Karkashin wancan umarni da shugaba Tinubu ya bayar, rahotanni sun nuna cewa kawo yanzu jami’an soji sun samu nasarar kama wasu da ake zargi da aikata laifin.

Al’umma da dama ne suka tsere daga gidajensu a yankin da lamarin ya faru, bayan da wasu rahotanni suka zargi sojoji da kai harin ramuwar gayya, zargin da tuni rundunar sojojin Najeriya ta musunta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.