Gwamnan Kaduna ya mika daliban Kuriga ga iyayensu
Gwamnan jihar Kaduna da ke Najeriya, Sanata Uba Sani ya mika daliban makarantar Kuriga ga iyayensu bayan sun shafe kimanin sa'o'i 48 a hannun gwamnati ana kula da lafiyarsu sakamakon wahalar da suka sha a hannun 'yan bindigar da suka yi garkuwa da su.
Wallafawa ranar:
Gwamnan ne ya sanar da mika daliban a shafinsa na Facebook a wannan Alhamis, yana mai cewa, ya mika daliban cikin sosuwar zuciya.
Gwamnan ya tabbatar cewa, sai da aka tabbatar da cikakkiyar lafiyar jiki da ta kwakwaluwar daliban kafin yanke shawarar mika su ga iyayensu da suka dade cikin zumudin haduwa da yaran nasu.
Gwamnan ya kara da cewa, daliban wadanda ya dauka a matsayin 'ya'yansa na ciki sun yi masa alkawarin cewa, za su mance da mummunar jarrabawar da ta same su tare da mayar da hankali kan karatunsu.
Domin nuna godiya kan jajircewar da yaran suka nuna, da kuma tsayin-dakarsu kan cimma burinsu na neman ilimi duk da mummunan ibtila'in da ya same su, gidauniyar Uba Sani za ta dauki nauyin karatunsu har zuwa matakin makarantar gaba da sakandare.
A bangare guda, gwamnan na Kaduna ya yi alkawarin cewa, zai biya diyya da iyalan Malam Abubakar wanda ya rasa ransa a hannun 'yan bindigar da suka kaddamar da farmaki kan makarantar ta Kuriga, inda gwamnan ya ce, zai bai wa iyalan nasa diyyar naira miliyan 10.
Sannan gwamnatin Kaduna za ta dauki nauyin karatun 'ya'yansa har zuwa matakin makarantar gaba da sakadanre kamar yadda sanarwar ta shafin Facebook ta yi karin bayani.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu