Matsalar 'yan bindiga ta raba sama da mutum dubu 300 da muhallansu a Kaduna
Akalla mutane kusan dubu dari uku ne hare-haren 'yan bindiga ya raba su da muhallansu a garurruka 551 a cikin kananan hukumomi goma sha biyu a jihar Kaduna.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kunna - 03:07
Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar ce ta bayyana haka a lokacin da take rabon kayan abinci ga wadanda lamarin ya rutsa da su a karamar hukumar Kajuru.
Jihar Kaduna dai na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke fama da matsalar 'yan bindiga da suke garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken rahoton Aminu Sani Sado.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu