Isa ga babban shafi

Tinubu ya bukaci 'yan Najeriya su hada kansu don ciyar da kasar gaba

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bukaci ‘yan kasar da su hada kansu da kuma nuna halin sadaukar wa, don gudanar da aikin gina kasar.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu. REUTERS - TEMILADE ADELAJA
Talla

A cikin sakonsa na barka da Sallah da mai taimaka masa wajen hulada da kafafen yada labarai Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce wannan lokaci ne na mai da lamura wajen Ubangiji, don haka ya kamata al’ummar kasar su dukufa wajen samar da hadin kai a tsakaninsu.

Shugaba Tinubu wanda ya taya al’ummar Musulmin Najeriya da ma duniya baki daya murya, ya kuma yi addu’ar Allah ya amshi ibadun da suka gabatar.

Sakon babban hafsan sojojin kasa na Najeriya

Shima a nasa sakon barka da sallah, babban hafsan rundunar sojojin kasa na kasar Janar Taoreed Lagbaja, ya bukaci dakarun kasar da su rubanya kokarin da suke yi wajen yaki da matsalar tsaro a fadin kasar.

Babban hafsan rundunar sojojin kasa na Najeriya Janar Taoreed Lagbaja.
Babban hafsan rundunar sojojin kasa na Najeriya Janar Taoreed Lagbaja. © Daily Trust

Janar Lagbaja ya kuma ce irin kokarin da  suke yi a yaki da ‘Yan ta’adda da ‘Yan bindiga da kuma ayyukan barayin man fetur ba zai tafi kawai ba, ya na mai jaddada bukatar da ke akwai ga Jami’an wajen kara kaimi a ayyukan da suke yi na wanzar da zaman lafiya a Najeriya.

Kazalika ya bukaci Dakarun kan su hada karfi da karfe da sauran jami’an tsaro wajen gudanar da ayyukansu na kakkabe masu kawo tazgaro ga tsaron kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.