Isa ga babban shafi

'Yan bindiga da Boko Haram sun yashe dukiyar al'ummar garin Allawa a jihar Neja

A Najeriya ‘yan bindigar daji da hadin gwiwar mayakan Boko Haram sun kai farmaki kan garin Allawa na karamar hukumar Shiroro a jihar Neja, kwanaki bayan janyewar Sojojin kasar bayan kulle wani karamin sansaninsu da ke aikin bayar da tsaro ga al’ummar yankin.

'Yan bindiga sun addabi wasu jihohin Najeriya
'Yan bindiga sun addabi wasu jihohin Najeriya © dailypost
Talla

Shaidun gani da ido sun tabbatarwa sashen Hausa na RFI yadda ‘yan ta'addan suka shiga garin da babbar motar diban kaya inda suka rika yashe kayan abinci da dabbobi da ma sauran muhimman abubuwan bukata.

Wannan lamari dai na zuwa ne kwana 3 tsakani bayan karamin sansanin Sojin Najeriya ya bar garin na Allawa sakamakon tsanantar hare-haren ‘yan bindiga da a lokuta da dama kan kai ga asarar tarin dakarun.

Tun bayan janyewar Sojoji daga garin na Allawa ne, al’umma suka rika ficewa don samun mafaka ko dai a makwabta ko kuma wasu garuruwan da ke wajen jihar mai fama da hare-haren ‘yan ta’adda.

Babu dai rahoton da ke tabbatar da rasa rayuka a harin na yammacin jiya Lahadi lura da cewa 'yan ta'addan basu samu ko da mutum guda a cikin garin da kauyukan da ke zagaye da shi ba, sai dai lamarin ya firgita al’ummar da ke makwabtaka da garin wadanda suka shiga dimuwa tun bayan ficewar dakarun Sojin Najeriyar daga garin na Allawa.

Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken rahoton da wakilinmu Isma'il Karatu Abdullahi ya hada mana daga jihar Neja.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.