Isa ga babban shafi

Sharhin masana kan ƴunƙurin Najeriya da Japan na yaƙar matsalar tsaro a Sahel

Najeriya ta sanar da kulla wata yarjejeniyar tsaro tsakaninta da Japan wadda za ta baiwa kasashen biyu damar yin hadin gwiwa a wajen yaki da matsalolin tsaron da suka addabi kasashen yankin Sahel.

Ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Tugga da takwararshi ta Japan Kamikawa Yoko.
Ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Tugga da takwararshi ta Japan Kamikawa Yoko. © dailytrust
Talla

Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya da ke sanar da kulla wannan yarjejeniya ta ce aikin yaki da matsalolin tsaron na hadaka tsakaninta da Japan zai shafi kasashen da suka kunshi Nijar da Chadi da Sudan da Senegal baya ga Sudan ta kudu da kuma jamhuriyyar tsakiyar Afrika sai Mali da Burkina Faso kana Mauritani baya ga ita kanta uwar gayya Najeriyar.

Matsalolin tsaro

Wata sanarwar hadaka tsakanin Japan da Najeriya wadda ma’aikatar wajen Najeriyar ta fitar bayan ganawar kwanaki biyu tsakanin wakilan kasashen, ta ruwaito ministan harkokin wajen Najeriyar Yusuf Tuggar na cewa kasashen biyu za su yi aiki ne don warware tushen matsalolin da suka haddasa rashin tsaro a kasashe na Sahel da ma ta’addancin kungiyar Boko Haram da ya wargaza tsaron yankin arewa maso gabashin kasar.

A bangare guda ministar harkokin wajen Japan, Ms Kamikawa Yoko, ta bayyana cewa kasashen biyu sun aminta da hada karfi don magance matsalolin tsaron da ke barazana ga kasashen yankin Sahel, kuma ko shakka babu Tokyo za ta bayar da dukkanin tallafin da ake bukata wajen samar da zaman lafiya a kasashen.

Wasu bangarorin yarjejeniyar

Haka zalika Miss Kamikawa ta bayar da tabbacin zuba jari a wasu birane na Najeriya baya ga bayar da gudunmawa wajen tabbatar da ‘yancin mata wayar da kai da kuma habaka tattalin arziki.

Bayanai na nuna cewa Japan na shirin fadada bangarorin kera-keran fasahar zamani a sassan Najeriya, kasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afrika.

Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraren abin da Farfesa Usman Mohammed na cibiyar horas da ƴan majalisa a Abujan Najeriya ke cewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.