Isa ga babban shafi

Dillalan man fetur kusan dubu 9 ke gab da rasa lasisin su a Najeriya

Najeriya – Akalla dillalan man fetur dubu 9 ne a Najeiya ke gab da rasa lasisin cinikayyar su a kasar sakamakon rashin sabunta ta su, sakamakon kawo karshen wa'adin da kamfanin NNPC ya gindaya musu.

Shugaban kamfanin man fetir ɗin Najeriya Alhaji Mele Kolo Kyari. 28/03/24
Shugaban kamfanin man fetir ɗin Najeriya Alhaji Mele Kolo Kyari. 28/03/24 © Mele Kyari X
Talla

Yanzu haka dillalan ta hannun kungiyar su ta IPMAN ta gabatar da roko na musamman ga kamfanin NNPC da ya yiwa Allah wajen tsawaita wa'adin sabunta lasisin har zuwa karshen watan Yuli mai zuwa.

Dillalan sun kuma roki hukumar dake kula da lasisin a karkashin NNPC da ta gaggauat sakin lasisin da aka sabunta ga wadanda suka samu nasara.

Babban jami'in hulda da jama'a na kungiyar dillalan Chinedu Ukadike ya gabatar da wannan bukata a takardar da ya rabawa manema labarai.

Yanzu haka 'yan Najeriya na fuskantar matukar wahala wajen samun man fetur a gidajen mai saboda karancin sa, abinda ya haifar da dogayen layuka a biranen kasar tare da tsadar sa a kasuwannin bayan fage ko kuma hannun 'yan bumburutu.

Kamfanin NNPC da kungiyar dillalan man na zargin juna da haifar da karancin man wanda ya jefa rayuwar jama'ar kasar cikin halin kakanikayi.

Masu bukatar man da dama sun koma kwana a gidajen mai domin samun sa a farashi mai sauki ko kuma sayen sa ad tsada a hannun 'yan bunburutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.