France
Mutane 15 suka mutu a Faransa sanadiyyar ambaliya
Mamakon ruwan sama da aka kwarara kamar da bakin kwarya a kudancin kasar Faransa ya haddasa mummunar ambaliya da ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 15, wasu da dama suka bace bat.Daruruwan mutane suka sami agajin jami’an kashe gobara, bayan da ruwan ya rutsa dasu a cikin gidaje da motoci da kuma kan rufin gine-gine.Dole sai da aka dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa daga Toulon zuwa Saint- Raphael, kuma jirage masu saukar angulu ne ke ceton rayukan mutane zuwa garin Draguignan, dake da yawan mutane dubu 40 in an doshi tsibirin kogin Meditareniya.
Wallafawa ranar: