Isa ga babban shafi
Rasha-Turai

Putin ya gargadi kasashen Yammaci domin kaucewa tsoma baki ga siyasar Rasha

Fira Ministan kasar Rasha, Vladimir Putin, ya gargadi kasashen Turai da su kaucewa tsoma bakinsu a siyasar kasar, yayin da yake jawabin amincewa tsayawa takarar shugabancin kasar a shekara mai zuwa.

Fira Ministan kasar Rasha, Vladimir Putin lokacin da yake jawabi bayan tsayar da shi takarar shugabancin kasar.
Fira Ministan kasar Rasha, Vladimir Putin lokacin da yake jawabi bayan tsayar da shi takarar shugabancin kasar. REUTERS/Sergei Karpukhin
Talla

Putin ya zargi kasashen Turai, wajen bai wa kungiyoyin fararen hula makudan kudade a cikin Rasha, don sauya ra’ayin mutane dangane da zabe mai zuwa, inda ya bayyana matakin a matsayin hasarar kudi.

A cewar Mista Putin ya dace kasashen su yi amfani da kudin domin magance matsalar bashin da ke addabarsu ba wai bata lokaci ba ga shiga harakar wata kasa.

Jam’iyyr Putin ta amince da Putin ne bayan samun rinjayen kuri’u, kuma wannan na zuwa ne bayan shugaban kasar Dmitry Medvedev yace a watan Satumba zai yi murabus daga mukamin shugaban kasa.

Putin ya kwashe tsawon shekaru yana taka muhimmiyar rawa a siyasar kasar Rasha tun bayan day a karbi mulki hannun Boris Yeltsin a shekarar 2000 bayan samun Soviet, a shekarar 2008 ne kuma ya mika mulki ga Medvedev bayan ya kwashe wa’adi biyu yana mulkin kasar.

Idan dai aka zabi Putin zai kwashe shekaru yana shugabancin kasar har zuwa shekarar 2024 inda zai kasance shugaban day a fi dadewa saman mulki a kasar Rasha bayan tsohon shugaban Soviet Josef Stalin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.