Isa ga babban shafi
Faransa-Algeria

Bukin tuna yakin Algeria a Faransa

Shekaru hamsin da suka gabata, ra’ayi ya banbanta tsakanin Faransawa game da yakin Algeria, da ya kawo karshe shekaru 132 da suka gabata a zamanin mulkin mallaka inda wasu ‘yan kasar ke gudanar da buki domin juyayin wadanda jami’an tsaro suka kashe a tashar jirgin kasa a birnin Paris domin neman zaman lafiya a Algeria.

Wasu masu zanga zanga a harabar filin saukar jirgin saman  Charles-de-Gaulle kusa da birnin Paris
Wasu masu zanga zanga a harabar filin saukar jirgin saman Charles-de-Gaulle kusa da birnin Paris Reuters/Gonzalo Fuentes
Talla

Shekaru 50 ke nan da ake wa kallon kisan ta fuska biyu a Faransa game da yadda za’a yi bukin ranar kawo karshen yakin kasar Algeria, wanda ya kawo karshen shekaru 132 Algeria na karkashin mulkin mallaka.

Magoya bayan tsarin gurguzu da ke Faransa na juyayin wannan rana ta yau, inda ‘yan sanda suka tarwatsa masu bore da aka haramtawa a tashan jirgin kasa na Charonne a Paris.

Wata tsohuwa mai suna Maryse Tripier, da shekaru 50 ‘Yar makaranta ce, tace an haramta masu yin bore da a wancan lokaci, amma suka shiga boren domin tunanin yana da wahala a kashe wasunsu.

Har yanzu babu bayanai game da yawan wadanda suka mutu, masana tarihi na cewa har yanzu Hukumomin kasar Faransa basu fito fili sun amsa sun yin laifi ba.

A bara ne dan takarar Shugabancin kasar Faransa a yanzu Francois Hollande, da magajin garin Paris Bertrand Delanoe suka mika ta’aziya ga mamatan da suka ce sun kai kimanin 200.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.