Isa ga babban shafi
Rasha-Ukraine

Putin da Poroshenko sun amince a tsagaita wuta a Ukraine

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Ukraine Petro Poroshenko  sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta mai dorewa a rikicin da ‘Yan a ware suka mamaye gabacin Ukraine. Shugabannin biyu sun amince da yarjejeniyar ne a zantawar da suka yi ta wayar tarho, kamar yadda gwamnatin Ukraine ta fitar da sanarwa.

Shugaban Rasha Vladimir Putin yana gaisawa da Shugaban Ukraine Petro Poroshenko  à Minsk
Shugaban Rasha Vladimir Putin yana gaisawa da Shugaban Ukraine Petro Poroshenko à Minsk REUTERS/Sergei Bondarenko/Kazakh Presidential Office/Pool
Talla

A ganawar da Putin na Poroshenko suka yi a Minsk a makon jiya an tashi ne baran baran ba tare da sun amince da matakan samun zaman lafiya ba, bayan kwashe lokaci gwamnatin Ukraine na zargin Rasha da taimakawa ‘Yan tawaye da ke kishinta.

Rasha ta musanta duk wani zargi da ake yi akan ta aika da Sojoji zuwa Ukraine domin taimakawa ‘Yan tawaye a gabacin kasar.

Amincewa da yarjejeniyar na zuwa ne a yayin da kasar Rasha ke bayyana damuwa akan matakan da kasashen Yammaci suka dauka akanta.

Rasha ta bayyana kungiyar kawancen tsaro ta NATO a matsayin babbar barazana bayan kasashen Yammacin duniya sun sanar da shirin karafafa matakan tsaro a gabashin Turai saboda takalar da suka ce Rasha na yi a Ukraine.

A Gobe ne za’a gudanar da taron kungiyar NATO a Wales, inda ake saran shugaba Petro Poreshonko zai lallashi shugaba Barack Obama don samun taimakon soji.

Majalisar Dinkin Duniya tace kimanin mutane 2,600 aka kashe a rikicin da ake yi a gabacin Ukraine tsakanin ‘Yan a ware da gwamnatin kasar. Rahoton yace adadin mutane 2,593 aka kashe tsakanin Watan Afrilu zuwa Agusta na wannan shekarar ta 2014.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.