Isa ga babban shafi
Girka-EU-IMF

IMF ta gindayawa Girka sharadi

Hukumar bayar da lamuni ta duniya IMF ta bayyana aniyarta na kauracewa sabon shirin tallafawa kasar Girka da bashi, karo na uku a jere, matsawar Girka ta ci gaba da dagewa kan sharuddan da ta kasa cim ma matsaya a kansu tsakaninta da kungiyar Tarayyar Turai.

Shugabar IMF Christine Lagarde
Shugabar IMF Christine Lagarde Reuters
Talla

Girka ta bukaci soke wani kaso daga cikin basukan da ta hada daga kasashen Turai da sauran masu ba ta bashi, kamar yadda wani babban jami’in hukumar ta IMF ya bayyana.

Wannan kuma na zuwa ne a yayin hukumomin da ke bin Girka bashi da suka hada da hukumar Tarayyar turai da babban Bankin Turai suka soma tattauna a Athens domin shirin ba Girka wasu karin tallafin kudi yuro biliyan 86.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.