Isa ga babban shafi
Faransa-Coronavirus

Faransa za ta rika killace 'yan Birtaniya saboda corona

Faransa ta bijiro da sabuwar dokar da za ta tilasta wa bakin da ke shiga kasar daga Birtaniya killace kansu na tsawon makwanni biyu don kare yaduwar cutar corona. Kakakin gwamnatin kasar Gabriel Attal ne ya bayyana hakan, inda ya ce dole ne Faransa ta yi duk mai yiwuwa wajen kare jama’arta daga cutar ta Covid-19.

Wasu fasinjojin jirgin sama
Wasu fasinjojin jirgin sama AP - Jerome Delay
Talla

Da yake zantawa da manema labarai, Gabriel Attal ya ce, an dauki wannan mataki ne a yayin zaman majalisar zartaswa ta kasar, sai dai ya ce baya ga killacewar ma, akwai wasu matakai da za a dauka wanda za a bayyana su nan gaba kadan.

Tuni Jamus ta dauki makamancin wannan mataki na hana jama’a daga Burtaniya shiga kasar kai tsaye, a cewarsu ana yawan samun mutanen da ke zuwa kasar daga Burtaniya dauke da cutar.

Baya ga Birtaniyar, Faransan ta dauki makamancin wannan mataki kan kasashe irinsu Brazil da India da Argentina da Chile da Afrika ta Kudu da kuma Colombia.

Sauran sun hada da Uruguay da Costa Rica da Bahrain da Turkiya da Bangledesh da Sri Lanka da Pakistan da Nepal da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Qatar.

A wani rahoto da Hukumar Lafiya ta Duniya ta fitar a baya-bayan nan ta ce, nau’in coronavirus na kasar India ya fantsama a kasashe 53 na duniya, a don haka akwai bukatar kasashe su sanya idanu sossai kan shige da ficen jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.