Macron na ziyara a yankin da Faransa ta taba gwajin makamin Nukiliya
Shugaban Faransa Emmanuel Macron na fuskantar matsin lamba don neman gafara kan mummunan tasirin da gwajin nukiliya ya yi shekaru da dama dai-dai lokacin da ya fara ziyarar aiki ta farko zuwa yankin Polynesia da lamarin ya shafa.
Wallafawa ranar:
A ziyarar tasa ta kwanaki hudu, Macron zaiyi kokarin kwantar da hankulan al’ummar yankin kan batun na gwajin makamin nukiliya daga shekarar 1966 zuwa 1996, wato lokacin da Faransa ta kera makamin Nukiliya.
Macron zai kuma tattauna muhimmiyar batutuwa da suka hada rawar da yankin dake kudu maso gabashin tekun Pacific ke da shi, da kuma batun dumamar yanayi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu