Isa ga babban shafi

An kashe fiye da Euro biliyan biyu a ciniki ko musayar 'yan wasa a Birtaniya

Kamfanin Deloitte na Birtaniya ya bayyana cewa an kashe fiye da Euro biliyan biyu a ciniki ko musayar 'yan wasa a lokacin kaka. Gasar cin kofin Ingila ta yi kaca-kaca a kan kasuwar saye da sayar da yan wasa a lokacin guda kamr dai yada wannan bincike da reshen wasanni na kamfanin Deloitte na Birtaniya ya fitar.

Premier League.
Premier League. © AFP - ADRIAN DENNIS
Talla

Masu sharhi kan al'amuran da suka jibanci wasannin kwallon kafa sun bayyana cewa duk da mawuyacin halin da ake ciki na tattalin arziki a Ingila - tare da hauhawar farashin kayayyaki, kungiyoyin firimiya ne 20 suka kashe Fam biliyan 1.9 kimanin Yuro biliyan 2.2, an zuba wadanan kudade a kan tebur don sayo 'yan wasa 169,cinikin da aka kammala da yammacin  jiya Alhamis a Turai, a cewar kamfanin.

A cewar Kamfanin Deloitte, wannan adadi ya shiga tarihi,wanda ya kuma haura kashi 67% idan aka kwatanta da kasuwar musayar 'yan wasa a shekara ta 2022.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.