Isa ga babban shafi

Ukraine ta kwace yanki mai fadin murabba'in kilomita dubu 6 daga Rasha

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce dakarun kasar sun karbe yankunan da fadinsu ya kai murabba’in kilomita dubu 6 daga hannun Rasha a cikin wannan wata kawai, a ci gaba da turjiyar da su ke yi dangane da mamayar da Moscow ke yi wa kasar.

Dakarun Sojin Ukraine bayan kwace iko da yankin Kupiansk daga hannun Rasha.
Dakarun Sojin Ukraine bayan kwace iko da yankin Kupiansk daga hannun Rasha. © REUTERS
Talla

Shugaban kasar ta Ukraine ya yi ikirarin samun nasara a martanin da su ke maidawa mamayar da Rasha ta yi musu a yankin Kharkiv da ke arewa maso gabashin kasar, inda ya ce dakarunsa sun kwato gwamman yankuna, ciki har da biranen Izyum, Kupiansk da Balakliya, garuruwa na farko farko da Rasha ta kwace.

Yayin jawabin da ya saba gabatarwa a kullum kan yakin da su ke gwabzawa da Rasha, Zelensky ya ce tun daga farkon watan Satumba, sojojin Ukraine sun 'yantar da yankunan Ukraine da fadinsu ya kai murabba'in kilomita 6,000 a gabashi da kudancin kasar, kuma dakarun nasa na cigaba da dannawa domin kwato ragowar yankunan da ke karkashin sojojin Rasha.

Shugaban na Ukraine ya kuma yi ikirarin samun gagarumar nasara a yankin kudancin Kherson, inda sojoji suka ce sun sake kwato yankin da fadinsa ya kai murabba'in kilomita 500.

Tun daga ranar 24 ga watan Fabarairun da ya gabata ne, Rasha ta fara kaddamar da hare-hare a sassan Ukraine bisa wani yunkuri na kwace yankuna da ke amfani da harshen Rashanci wadanda ke karkashin ikon Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.