Isa ga babban shafi

Rasha ta ce shugaba Putin ya ziyarci Mariupol duk da sammacin kama shi na ICC

Fadar Kremlin ta ce shugaban Rasha Vladimir Putin ya kai wata ziyarar bazata birnin Mariupol bayan da ya kammala ziyartar Crimea don gudanar da bikin cika shekaru 9 da mamayar tsibirin, wanda tun asali malllakin Ukraine ne.

Shugaban Rasha, Vladimir Putin tare da mataimakin Fira Minista,. Marat Khousnoulline  a yayin da suka isa birnin Mariupol a ranar Lahadi, 19 ga watan Maris, 2023.
Shugaban Rasha, Vladimir Putin tare da mataimakin Fira Minista,. Marat Khousnoulline a yayin da suka isa birnin Mariupol a ranar Lahadi, 19 ga watan Maris, 2023. AP
Talla

Wannan ce  ziyarar Putin ta farko zuwa yankin Donbas na Ukraine da Rasha ta mamaye tun da aka fara yaki tsakanin kasashen biyu a watan Fabrairun bara.

Ziyarar ta Vladimir Putin zuwa wannan birni na Mariupol na zuwa ne kwanaki biyu bayan da kotun hukunta manyan  laifuka ta ICC ta bada sammacin a kamo mata shi, bisa zarginsa da kwashe kanan yaran Ukraine zuwa Rasha ba bisa ka’ida ba.

Kafofin yada labaran Rasha sun ruwaito mataimakin Fira Ministan Rasha Marat Khusnullin na cewa al’ummar Mariupol sun fara komawa birnn sannu a hankali.

Mariupol na da yawan al’umma da ya kai rabin miliyan gabanin yakin da aka fara a shekarar 2022, kuma nan ne kamfanin sarrafa karafa na Azovstal yake.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.