Isa ga babban shafi

Super Eagles za ta hadu da kasashen Ghana da Mali a wasannin sada zumunta

Super Eagles ta Najeriya ta fitar da sunan jerin ‘yan wasan da za su wakilce ta a wasannin sa da zumuntar da ke tunkarota wanda za ta kara da kasashen Ghana da kuma Mali a watan nan.

Tawagar Super Eagles ta Najeriya.
Tawagar Super Eagles ta Najeriya. AP - Sunday Alamba
Talla

A ranar 22 ga watan nan ne Super Eagles za ta fuskanci Ghana a wasan sada zumunta, yayinda za ta hadu da Mali a ranar 26 ga watan nan, kuma dukkanin wasan babu wanda zai zowa tawagar da sauki duk da cewa dai wasanni ne na sada zumunta.

Wasannin za su kasance na farko da tawagar za ta doka ba tare da mai horar da ita Jose Peseiro ba, wanda ya kaita wasan karshe na cin kofin Afrika a Ivory Coast cikin watan jiya.

Haka zalika wasan na zuwarwa Super Eagles dai dai lokacin da ta ke da tarin ‘yan wasan da yanzu haka ke jinyar rauni.

Sai dai wani sako da NFF ta wallafa a shafinta na X ya bayyana sunayen ‘yan wasan irinsu Cyriel Dessers da Nathan Tella da kuma Simon Moses da Nwabali Stanley baya ga Fisayo Bashitu da Calvin Bassey da kuma Iwobi Alex baya ga Semi Ajayi da Jamilu Collins sai Bruno Onyemaechi da Sadiq Umar a matsayin wadanda za su wakilci tawagar.

Yanzu haka dai ‘yan wasan Najeriyar da ke jinyar rauni sun kunshi Victor Osimhen da Gabriel Osho da Tyronne Ebueh da kuma Taiwo Awoniyi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.