Isa ga babban shafi

Masu shigar da kara a Spain sun nemi kotu ta aike da Rubiales gidan yari

Masu shigar da kara a Spain na bukatar kotu ta yankewa tsohon shugaban hukumar kwallon kafar kasar Luis Rubiales wa’adin zaman shekaru 2 da rabi a gidan yari, duk dai dangane da sunbatar ‘yar wasa Jenni Hermoso cikin watan Agustan da ya gabata.

Tsohon shugaban hukumar kwallon kafar Spain Luis Rubiales.
Tsohon shugaban hukumar kwallon kafar Spain Luis Rubiales. AP - RFEF
Talla

Idan ba a manta ba dai, jim kadan bayan da tawagar Mata ta Spain ta lashe kofin duniya ne Rubiales ya sumbaci kyaftin din tawagar wato Hermoso, sunbatar da ta ja mishi rasa aikinsa baya ga fuskantar tuhuma kan cin zarafi.

Duk da cewa har zuwa yanzu Rubiales na ci gaba da musanta cewa da nufi ne ya sumbaci Hermoso, sumbatar da ta sabawa ka’ida, amma ‘yar wasa da abokananta na tawagar kasar na neman lallai kotu ta yi mata adalci domin kuwa yanayin sumbatar ba wai farin ciki ne ya kawo shi ba, face yunkurin cin zarafi.

Cikin takardun da masu shigar da karar suka gabatar gaban kotun ta Spain sun nemi daure Rubiales kan laifin cin zarafin ‘yan wasa sai kuma kocin tawagar Jorge Vilda da Albert Luque daraktan wasanni na tawagar baya ga Ruben Rivera shugaban tsare-tsare na tawagar wadanda suma aka nemi yanke musu zaman wa’adin, bayan samunsu da laifin tilastawa Hermoso amsa cewa sumbatar da Rubiales ya yi mata ba komi bace.

Dukkanin mutanen 4 dai za su biya tarar yuro dubu 100 kowannensu baya fa daurin akalla watanni 18 zuwa sama a gidan yari matukar kotun ta tuhumesu kan abin da masu shigar da karar suka bukata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.