Isa ga babban shafi

An sake dakatar da Sandro Tonali daga wasanni saboda caca

Hukumar kwallon kafar Ingila ta dakatar da dan wasan Newcastle United, Sandro Tonali na watanni biyu, sakamakon karya dokar yin caca.

Dan wasan Newcastle Sandro Tonali
Dan wasan Newcastle Sandro Tonali AP - Scott Heppell
Talla

Dan kasar Italiya, mai shekara 23, na cikin hukuncin dakatarwar wata 10 da aka yanke masa cikin Oktoban 2023, bayan da ya aikata laifin a Italiya, lokacin yana taka leda a AC Milan.

Cikin watan Maris hukumar kwallon kafar Ingila ta tuhumi dan wasan da cewar ya yi caca 40 zuwa 50 bayan da ya koma Newcastle daga AC Milan a watan Yuli, ciki har da yi a kan sakamakon wasannin kungiyar St James Park.

A watan Oktoban 2023 ma Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Italiya (FIGC) ta dakatar da ɗan wasan tsakiyar na tsawon wata goma saboda saɓa ka’idojin caca.

Tonali ya koma Newcastle ne daga AC Milan a watan Yulin 2023 kan fam miliyan 55.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.