Isa ga babban shafi

Majalisar Dokokin Najeriya ta amince da sabuwar dokar bai wa dalibai bashin karatu

Majalisar Dokokin Najeriya ta amince da dokar bai wa dalibai bashin karatu a manyan makarantun kasar, wadda ta sha caccaka a baya.

Wasu daliban Jami'a a Najeriya.
Wasu daliban Jami'a a Najeriya. The Guardian Nigeria
Talla

Wannan dai na a matsayin gyara da kuma sake amincewa da ita, kasancewar a baya ‘yan majalisar sun amince da ita, amma daga bisani aka gano kura-kurai a cikinta.

Shugaban kasar Bola Ahmad Tinubu ne ya bijiro da dokar tare da mika wa ‘yan majalisar don amincewa da ita.

Dokar ta kunshi bai wa dalibai bashin kudade don biyan kudin makaranta da sauran bukatun yau da kullum da suka shafi karatunsu, inda za su fara biya da zarar sun kammala karatu, sun sami aikin yi ko kuma sun kama sana’a.

Sai dai kuma tun a wancan lokaci kungiyoyin dalibai da na fararen hula suka fara caccakar sabuwar dokar, a ganinsu tamkar bautar da dalibai ne a fakaice, ma’ana dai a maimakon su fara amfani da albashinsu wajen gina rayuwa bayan samun aiki sai su bige da biyan gwamnati bashi.

A maimakon haka kungiyoyin na ganin kamata ya yi gwamnati ta sassauta kudaden makaranta ta yadda kowa zai iya biya da kudin aljihunsa ba tare da karbar bashi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.