Isa ga babban shafi

Trump da mukarrabansa na fuskantar tuhumar yunkurin jirkita sakamakon zabe

Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump na fuskantar  zarge-zarge da suka hada laifukan da suka shafe  zabe bayan da aka shafe shekaru biyu ana gudanar da bincike a kan yunkurin da ya yi na karkata  akalar sakamakon zaben da ya nuna cewa ya sha kashi a hannun dan takaran jam’iyyar Democrats, Joe Biden.

Tsohon shugaban Amurka,  Donald Trump.
Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump. AP - Artie Walker Jr.
Talla

i

Masu gabatar da kara a Atlanta sun zargi  Trump da aikata manyan laifuka 13, abin da ya kara jefa shi cikin matsaloli a gaban kuliya, kuma ya saka burinsa na neman shugabancin kasar a karo na biyu cikin hatsari.

Wasu Karin mutane 118 suna fuskantar wadannan tuhume -tuhume  a kan wannan bincike da ake gudanarwa, ciki har da lauyansa, Rudy Giulianni, wanda  yake da hannu wajen matsa lamba a kan sakamakon zaben shekarar 2020, da kuma shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar Amurka, Mark Meadows.

Trump, tare da sauran wadanda ake zargi  sun ki amincewa da cewa Trump ya fadi zabe, kuma da gangan suka rika shiga cikin kulla  munakisar sauya sakamakon zaben ta inda zai nuna cewa shi Trump din ne ya ci zabe, kamar yadda takardar zargin ta bayyana.

Lauyoyin da aka ambaci sunayensu a kan wannan dambarwa sun ki cewa uffan, wasu daga cikinsu kuma ba a same su ba don  yi wa manema labarai bayani.

Wannan  batu da ya ke nema ya kai Trump ya baro dai ya samo asali ne daga zantawa ta wayar tarho da tssohon shugaban ya yi da shugaban hukumar zaben jihar Georgia, Brad Raffensperger,  inda  yake bukatar sa ya yi aringizon kuri’u da za su goge rashin nasarar da ya yi a jihar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.