Isa ga babban shafi

'Yan tawayen Houthi sun yi barazanar mayar da zazzafar martani bayan harin Amurka

'Yan tawayen Houthi sun yi barazanar mayar da zazzafar martani biyo bayan harin baya bayan nan da Amurka ta kaddamar a Yemen, wanda ya kara tada hankulan alumma. 

Masu zanga zanga a Yemen
Masu zanga zanga a Yemen REUTERS - DAVID RYDER
Talla

Amurka ta sha alwashin kare jiragen ruwan dakon kaya da ke ratsa tekun Bahar Maliya, daga hare haren dakarun dake marawa Iran baya. 

Hare haren na kara jefa fargabar cigaba da yaduwar rikicin gabas ta tsakiya, tun bayan Israila da Hamas suka soma yakin da ya ki ci ya ki cinyewa, inda wadanda ke marawa israilan baya ke amfani da wannan dama wajen kutsa kai daga kasashen Lebanon da Syria da kuma Iraqi.

Yayin zantawarsa da manema labarai, Shugaba Joe Biden ya ce Amurka ta aika sako na musamman zuwa ga Iran dangane da hare haren da mayakan Houthin ke kai wa, inda ya kara jaddada cewa a shirya kasar take. 

Harin baya bayan nan da Amurka ta kai na zuwa ne kwana guda bayan makamancinta da Birtaniya da ita kanta Amurkan suka kai a kan sansanonin mayakan Houthi din, saidai kakakin yan tawayen Houthin Nasruldeen Amer da ya tabbatarwa manema labarai batun harin, ya ce babu wanda ya jikkata kuma babu dukiyar da ta salwanta, amma a cewarsa dole su sun mayar da martani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.