Isa ga babban shafi

Tattaunawar cinikin makamai ta yi nisa tsakanin Rasha da Korea ta Arewa- Amurka

Amurka ta yi ikirarin cewa shugaba Kim Jong Un na Korea ta Arewa na shirin kai wata ziyara Rasha da nufin fara tattaunawar cinikayyar makamai tsakanin kasashen biyu, ko da ya ke fadar Kremlin ta ki yin karin bayani game da wannan ikirari.

Wata ganawar Kim Jong Un da Vladimir Putin na Rasha.
Wata ganawar Kim Jong Un da Vladimir Putin na Rasha. © Yuri Kadobnov / AP
Talla

Wannan ikirari na Amurka na zuwa kasa da mako guda bayan Washington ta gargadi Korea ta Arewa kan yunkurin sayarwa Rasha makamai, dai dai lokacin da Moscow ke laluben makaman da za ta ci gaba da yakin da ta ke a Ukraine.

Ko a farkon makon nan sai da shugaba Vladimir Putin ya bayyana ci gaba da hare-haren Ukraine kan yankunan kudanci da gabashi a matsayin babbar gazawar Sojin Rasha, wanda ke nuna yadda shugaban ya kagu matuka wajen ganin kasar ta samu tallafin kayakin yaki don karfafa dakarunta da ke fagen daaga.

Sai dai fadar Kremlin ta ki bayar da tabbacin ganawar ta Kim da Putin, duk da cewa kakakin majalisar tsaron fadar White House Adrienne Watson ta nanata cewa tabbas tattaunawa tsakanin Korea ta Arewa da Rasha ta yi nisa game da cinikayyar makaman.

Washington ta bayyana cewa tuni shugaba Kim Jong Un ya shiryawa ziyara a Moscow wadda ake sa ran ya yi amfani da jirgin kasan Soji da baya jin harsashi wajen balaguron zuwa Vladivostok da ke gab da gabar ruwa mai gajeruwar tazara daga Korea ta Arewa.

Ko a bara sai da Rasha ta karbi bakoncin taron kasuwancin kasashen gabashin Turai a garin na Vladivostok wanda wakilan kasashe 68 suka halarta.

A watan Yulin da ya gabata ne ministan tsaron Rasha Sergei Shoigu ya kai ziyara Korea ta Arewan ziyarar da Washington ke cewa a ita ne aka tattauna sabuwar cinikayyar makaman kari kan makamai masu linzami da Korean ta sayarwa Wagner a shekarar 2022.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.