Isa ga babban shafi

Trump ya kama hanyar lashe zaben fidda gwani na Jam'iyyar Republican

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump na gab da lashe zaben fidda gwani na jihar New Hampshire, nasarar da ke share masa hanyar yiwuwar samun damar tsayawa Jam’iyyar Republican takara a babban zaben kasar da ke tafe cikin shekarar nan.

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump da ke neman sake yiwa jam'iyyar Republican takara a zaben da ke tafe a bana.
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump da ke neman sake yiwa jam'iyyar Republican takara a zaben da ke tafe a bana. REUTERS - MIKE SEGAR
Talla

Zuwa yanzu fiye da kashi 80 na kuri’un aka kada kuma Trump ke jagoranci da fiye da rinjayen kashi 11 dai dai lokacin da babbar abokiyar karawarsa Nikki Haley ke shan alwashin ci gaba da jan hankalin masu kada kuri’ar don zabenta.

A wani jawabi da ya gabatar bayan bayyana kansa a matsayin Wanda ya yin asara, Trump mai shekaru 77 ya yi kira da Haley da ta koma gidanta a can jihar South Carolina domin kuwa shi ne mai nazara a tseren.

Trump wanda ya ci gaba da nanata cewa shi ne fa ya lashe zaben Amurka na 2020 ya sanya kudirin shige-da-fice a matsayin babban batu da zai mayar da hankali akai idan ya kai ga nasara hawa kujerar mulkin kasar.

Sai dai Haley ta bayyana cewa tsugune fa bata karewa Jam’iyyar ta Republican ba matukar ta tsayar da Trump a matsayin dan takara lura da yadda Democrats ke shirin amfani da abin kunyar da ya aikata wajen kayar da shi a zaben.

A cewar Nikki Haley, Democrats nada masaniyar cewa akan Trump ne kadai za su iya nasara amma baita ba.

Tun gabanin kammala zaben wanda aka faro kada kuri’ar daga daren jiya Talata zuwa wayewar garin yau Laraba, shugaba Joe Biden ya bayyana yiwuwar Trump ya iya nasara, wajen zama abokin karawarsa a zaben Amurkan da ke tafe a shekarar nan, kamar dai yadda suka fafata a 2020.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.