Isa ga babban shafi

Blinken zai gana da El-Sisi na Masar don kawo karshen yakin Isra'ila a Gaza

Sakataren wajen Amurka, Antony Blinken na gab da isa birnin Cairo na Masar a yau Talata don tattaunawa game da yiwuwar kawo karshen yakin Isra’ila a Gaza wanda aka shafe tsawon kusan watanni 5 ana yi da zuwa yanzu ya sanya fargabar sake rikecewar yankin Gabas ta tsakiya.

Antony Blinken na Amurka.
Antony Blinken na Amurka. © AFP
Talla

Zuwa yanzu Isra’ila ta kashe Falasdinawan da yawansu ya tasamma dubu 30 a luguden wutar da sojojinta ke ci gaba da y ikan rukunin gine-ginen gidajen fararen hula da asibitoci da masallatai a sassan Gaza.

Yayin ziyarar ta Blinken a yau, bayanai sun ce zai yi ganawa ta musamman da shugaba Abdel Fattah El-Sisi kwana guda bayan ganawarsa da Yarima mai jiran gadon sarautar Saudiya Mohammed bin Salman a birnin Riyadh.

Wannan ziyara dai na matsayin karo na 5 da Blinken ke kaiwa yankin na gabas ta tsakiya tun bayan faro yakin a ranar 7 ga watan Oktoban bara, wadda zai yada zango a Isra’ila da Qatar.

Ziyarar na zuwa a dai dai lokacin da Sojin Isra’ila ke fadada hare-harensu zuwa kudancin Rafah da ke da iyaka da Masar yankin da ke bayar da matsuguni ga falasdinawa kusan miliyan guda da Isra’ila ta kora daga muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.