Isa ga babban shafi

Akwai yiwuwar tsagaita wuta a Gaza gabanin watan Ramadana- Amurka

Shugaba Joe Biden na Amurka ya bayyana yiwuwar iya nasarar tsagaita wuta a yakin da Isra’ila ke yi a Gaza kafin kamawar watan Ramadana mai alfarma don bayar da damar musayar fursunonin bangarorin biyu.

Isra'ila na ci gaba da kisan fararen hular da basu ji ba basu gani a Gaza.
Isra'ila na ci gaba da kisan fararen hular da basu ji ba basu gani a Gaza. AP - Adel Hana
Talla

Kalaman na Biden a jiya Litinin na sake tabbatar da rashin goyon bayan Amurka wajen samar da yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin da nufin kawo karshen yakin na watanni 5.

Kafin kalaman na Biden dai bangarori da dama sun yi yunkuri tare da mabanbantan tattaunawa a kokarin dakatar da yakin wanda zuwa yanzu ya kashe Falasdianwa kusan dubu 30 baya ga jikkata wasu fiye da dubu 70.

Cikin kalaman na Biden a zantawarsa da gidan talabijin na NBC, ya bayyana cewa Isra’ila ta amince za ta dakatar da hare-harenta a cikin watan Ramadana don samun damar kubutar da ilahirin fursunonin da ke tsare a hannun Hamas.

Isra’ila dai na ci gaba da zafafa hare-hare a Rafah wanda ya sake tagayyara ayyukan jinkai a Gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.