Isa ga babban shafi

An samu koma bayan dimokradiyya a duniya - Rahoto

Wani bincike da aka gudanar a wata cibiya ta Amurka ya bayyana cewar dimokiradiya ta samu koma baya a wasu sassan duniya, sakamakon tashe tashen hankula da magudin zabe a shekarar da ta gabata.

Wani mutum kenan da ke jefa kuri'ar da ya kada cikin akwatin zabe a kasar Jamus, ranar 8 ga Oktoba, 2023.
Wani mutum kenan da ke jefa kuri'ar da ya kada cikin akwatin zabe a kasar Jamus, ranar 8 ga Oktoba, 2023. © Andreas Arnold / AP
Talla

Rahotan da Cibiyar bunkasa dimokiradiya ta ‘Freedom House’ ta gabatar, ya bukaci daukar matakai domin inganta tsarin shugabanci.

Rahotan shekara shekarar da Cibiyar ‘Freedom House’ ta fitar na shekarar 2023 yace, a karo na 18 a jere, tafarkin dimokiradiya ya samu koma baya ta yadda aka shake 'yancin siyasa da na bil adama a kasashe 52 na duniya, yayin da a kasashe 21 kawai aka samu ci gaba.

Yana Gorokhovskaia, daya daga cikin wadanda suka jagoranci rubuta rahotan tace, an samu wannan koma bayan ne a kowanne yanki na duniya.

Rahotan ya tabo batun juyin mulkin da sojoji suka gudanar a Jamhuriyar Nijar, wanda yake zuwa bayan na kasashen Burkina Faso, Chadi, Guinea, Mali da Sudan, yayin da kuma zabubbukan da aka gudanar a kasashe irin su Najeriya da Zimbabwe da kuma Madagascar suka bar baya da kura, sai kuma yadda tashin hankali ya yiwa 'yancin jama'a illa a kasashe irin su Sudan da Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo.

Shi dai wannan rahoto ya bayyana cewar nasarorin da dimokiradiyar ta samu a shekarar da ta gabata sun hada da zaben shugaban kasar Liberia, wanda aka kada shugaba mai ci da hukuncin kotuna a kasashen Kenya da Namibia, wadanda suka tabbatar da 'yancin 'yan luwadi da madigo.

Rahotan ya kuma tabo yadda shugabannin dake kan karagar mulki ke amfani da karfin ikon su wajen hana 'yan adawa rawar gabar hantsi a kasashe irin su Cambodia da Turkiya da Zimbabwe da Guatemala da kuma Poland.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.