Isa ga babban shafi

An mikawa Hamas tayin tsagaita wuta a gaza na tsawon kwanaki 40

Wakilan kungiyar Mayakan Hamas sun isa birnin Alƙahira a Masar, inda ake ƙoƙarin kullla yarjejeniyar tsagaita wutar yaƙin Gaza. Wannan na zuwa ne a yayin da Isra’ila ke cigaba kai hare-hare a sassan Zirin na Gaza, ciki har da Rafah, birnin da dakarun Isra’ila ke shirin afkawa da yaƙi ta ƙasa.

Palestinians carry aid as others struggle to receive their portion amid a widespread hunger, as the conflict between Israel and the Palestinian Islamist group Hamas continues, in Gaza City April 3.
Ko a safiyar yau Talata Isra'ila ta kai mabanbantan hare-hare Gaza tare da kashe tarin fararen hula. © REUTERS - Mahmoud Issa
Talla

A halin da ake ciki, Sakataren harkokin wajen Amurka David Cameroun ya ce an gabatar wa kungiyar Hamas tayin kullla yarjejeniyar kwanaki 40, tare sakin dubban Falasdinawan da Isra’ila ta kama a matsayin fursunoni, bisa sharaɗin cewar su ma mayakan na Hamas za su saki dukkanin ‘yan Isra’ilan da suka yi garkuwa da su.

Kasashen Masar da Amurka da Qatar ne ke ta kokarin shiga tsakani tattaunawar neman kulla yarjejeniyar tsagaita  wutar da ake yi kan yakin Gaza.

Sai dai har zuwa wannan lokaci Hamas ba ta ce komai kan tayin da aka gabatar mata, ko da ya ke dama kungiyar ta Hamas ta sha nanata gindaya sharuɗɗan cewa, ba za ta amince da ƙulla sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta ba har sai Isra’ila ta janye dakarunta baki ɗaya daga Zirin Gaza, ta kuma dakatar da kai hare-hare ta sama, don bai wa Falasɗinawa damar komawa tsirarun gidajen da suka rage ba a ragargaza su ba.

Wannan ya sa wasu masu sharhi ke kallon abin da kamar wuya, la’akari da alwashin Isra’ila a baya na cewar za ta samar da wani yankin tsaro a Gaza bayan kammala yaki da Hamas, don tabbatar da cewa ba a sake maimaita farmakin ranar 7 ga  watan Oktoban 2023 da mayakan Hamas suka kai mata.

A baya bayan nan kuma sakataren harkokin wajen Birtaniya David Cameroon ya ce muddin ana son cimma burin samar da kasar Falasɗinu to fa ya zama dole duk wani mai hannu a harin da aka kai wa Isra’ila a watan Oktoba ya fice daga Zirin Gaza, kuma dole a rushe duk wani abu da mayakan suka mallaka a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.