Isa ga babban shafi
RIKICIN ISRA'ILA DA HAMAS

Babu abin da zai hana mu kaddamar da hari a Rafah ta kasa - Netanyahu

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya nanata cewa sojojin Isra'ila za su kai farmaki ta kasa a Rafah, ko da anyi sulhu da Hamas ko kuma akasin hakan.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu kenan.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu kenan. REUTERS - RONEN ZVULUN
Talla

Netanyahu ya ce sojojin Isra’ila za su shiga Rafah domin kawar da ayarin dakarun Hamas.

A cewar sanarwar da ofishin firaministan ya fitar, dole ne a kwato dukkanin Yahudawan da suka rage a hannun Hamas, wadanda ta yi garkuwa da su a ranar 7 ga watan Oktoban bara.

Wani babban jami'in Isra'ila ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, gwamnati za ta jira har zuwa daren Laraba ya ce gwamnati za ta jira har zuwa daren Laraba game da matakin da Hamas za ta dauka game da batun tsagaita wuta.

"Isra'ila za ta yanke shawara da zarar Hamas ta bayyana matsayarta kan wannan yaki," in ji jami'in da ya nemi a sakaya sunansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.