Isa ga babban shafi

Ƴan sandan Amurka sun tarwatsa daliban da ke goyon bayan Falasdinawa

Ƴan sandan kwantar da tarzoma a Los Angeles sun tarwatsa sama da daliban Jami'ar California 400  wadanda ke zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasdinawa a wani sumame da suka kai wani sansani.

Yadda ƴan sandan Amurka suka kama ɗaya daga cikin ɗaliban jami'ar California masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa.
Yadda ƴan sandan Amurka suka kama ɗaya daga cikin ɗaliban jami'ar California masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa. AP - Ethan Swope
Talla

Ƴan sandan sun gudanar da samamen ne bayan da aka ba su umarnin tarwatsa daliban ko kuma a kama su a yau Alhamis.

Jami’an tsaron da ke kai kawo a kan manyan titunan California sun samu shiga wani bangare na sansanin da nufin kama masu zanga-zangar, sai dai sun bijirewa kamun.

Dalibai a jami’o’in Amurka daban-daban sun shafe kwanaki suna gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayansu ga Falasdinawa, koda a makon jiya ma sai da ƴan sanda suka tarwatsa wasu daliban a daidai lokacin da suke tsaka da gudanar da zanga-zangar.

Kazalika a ranar Juma’ar da ta gabata ma, zanga-zangar daliban Jami’a a birnin Paris na kasar Faransa ta ci gaba da bazuwa, bayan da ƴan sanda suka tarwatsa dandazon daliban a daren ranar Laraba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.