Isa ga babban shafi

Matsalar rashawa ke hana Amurka zuba jari a Najeriya - Blinken

A jawabinsa gaban taron manema labarai, sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken ya alakanta matsaloli masu alaka da rashawa baya ga wahalar canjin kudade a matsayin manyan dalilan da ke dakile masu zuba jari na Amurka iya gudanar da hada-hadarsu a Najeriya.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu, bayan karbar bakuncin Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a Abuja.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu, bayan karbar bakuncin Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a Abuja. AP - ANDREW CABALLERO-REYNOLDS
Talla

Blinken wanda ke ziyara a kasar mafi yawan jama’a kuma mafi karfin tattalin arziki a Afrika, ya bayyana cewa ko shakka babu Amurkawa na sha’awar zuba jari a Najeriyar amma tarin matsaloli ke hanasu iya aikata hakan.

A cewar Blinken baya ga daidaikun ‘yan kasuwa hatta kamfanoni musamman na bangaren fasaha da kere-kere na fatan samun damar shigowa Najeriyar don zuba jari, amma a lokacin da kasar ta bayar da damar shigowar masu zuba jari lamarin ya zo a dai dai lokacin da kasashen biyu ke kokarin kawo karshen wani kalubale da ke tsakaninsu da aka gaza shawo kansa tsawon lokaci.

Bayan ganawarsa da shugaba Bola Tinubu, Blinken ya shaidawa manema labaran cewa matukar Najeriyar na fatan samun zuba jari na kai tsaye tare da shigowar kamfanoni ko shakka babu sai ta yi aiki tukuru wajen magance matsalar cin hanci da rashawa wadanda za su bude hanya ga masu zuba jari su iya sauya kudadensu cikin sauki.

Najeriyar da Amurka dai sun sake sabunta kawancen da ke tsakaninsu ta fuskar tsaro tattalin arziki da kuma zuba jari har ma da ilimi da musayar fasahohi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.