Isa ga babban shafi
TSARO

Hukumomin tsaron Najeriya sun gayyaci Sheikh Ahmad Gumi

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa hukumomin tsaron kasar sun gayyaci fitaccen malamin addinin Islama nan da ke zaune a Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi domin amsa tambayoyi kan kalamansa game da ‘yan bindigar da ke addabar sassan arewacin kasar.

Sheikh Gumi a yayin ziyarar 'yan bindiga.
Sheikh Gumi a yayin ziyarar 'yan bindiga. © dailytrust
Talla

Ministan yada labarai, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugabancin kasar bayan zaman taron majalisar zartarwa ta tarayya.

Gumi dai ya tsaya tsayin daka wajen neman a yi wa ‘yan bindiga da ke addabar al'uma da kuma makarantu afuwa, inda ya nemi a yi zaman tattaunawa da su, domin a samu zaman lafiya, musamman a arewacin kasar.

Da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida a fadar Aso Rock, Idris ya ce, gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba domin samun irin bayanan da za su magance mata matsalolin tsaro.

Ya ci gaba da cewa, ba Sheikh Gumi ba, da duk wani wanda ke da masaniya akan ‘yan bindiga basu wuce doka ba, don haka idan akwai wanda yake da shawarwarin da ya kamata jami'an tsaro su dauka shakka babu za a gayyace shi.

“Babu wanda ya fi karfin doka kuma ina sane da cewa shi ma ba bako bane ga hukumomin tsaro domin amsa tambayoyi,” in ji Idris..

“Lokacin da kuke yin kalaman da suka dame mu kan  sha'anin tsaron kasa, ya zama wajibi ga hukumomin tsaro su kara zurfafa bincike a kan abin da zai haifar da rudani ga ‘yan Najeriya.”

Ministan ya kara da cewa, tun tuni ya kamata Najeriya ta rika gayyatar irin mutanen da ke da masaniya kan wadannan 'yan bindiga, domin nemarwa al'umma mafita game da halin da suke ciki na zaman dar-dar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.