Matsalar garkuwa da mutane na kara kamari a arewacin Najeriya
Wallafawa ranar:
Kunna - 10:19
A Najeriya an shiga wani yanayi na fargaba da kuma tsoro lura da yadda ‘yan bindiga suka tsananta dabi’ar yin garkuwa da mutane masu tarin yawa a lokaci daya musamman ma a yankin arewacin kasar.
A cikin makon da ya gabata kawai, sama da mutane 5,00 ne aka yi garkuwa da su, da suka hada mata ‘yan gudun hijira a jihar Borno, da daliban firamire da sakandare a jihar Kaduna, sai kuma almajiran tsagaya a jiyar Sokoto.
Abin tamabayar shine, shin me ke faruwa ne musamman ta la’akari da yadda hukumomin tsaro suka gaza bai wa jama’a kariya a sassan kasar?
Anya kuwa gwamnati na da wani tsari da za ta iya aiwatarwa don tunkarar wannan matsala?
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu