Isa ga babban shafi
Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

Kungiyoyin kwadago a Najeriya sun yi watsi da sabon harajin da CBN ya bullo da shi

Wallafawa ranar:

Ƙungiyar Ƙwadago da sauran kungiyoyin farar hula a Najeriya sun yi fatali da matakin gwamnati na baiwa bankuna umarnin fara cirar harajin kashi 0.5 wato rabin ɗaya kenan cikin 100, kan duk hada-hadar aika kudaden da ‘yan kasar ke yi ta intanet.

Najeriya:Gamayyar kungiyoyin kwadago ta fara gangamin adawa da janye tallafin mai
Najeriya:Gamayyar kungiyoyin kwadago ta fara gangamin adawa da janye tallafin mai © RFI
Talla

A cewar gwamnatin za a rika amfani da sabon harajin don samar da tsaro daga barazanar masu yi wa mutane kutsen satar kuɗaɗe da sauran muhimman bayanai ta shafukan intanet.

Sai dai ƙungiyoyin sun ce sabon harajin zai sake jefa ‘yan Najeriya musamman matsakaita da masu ƙaramin ƙarfi ne cikin ƙarin ƙunci, bayan matsin da suke ciki.

Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.