Najeriya: Ya zama wajibi a rika yiwa Malaman jami'o'i gwajin magunguna
Mataimakin shugaban jami’ar Abubakar Tafawa Balewa ATBU dake Bauchin Najeriya mai barin gado Professor Muhammad AbdulAziz, ya bayyana cewa ya kamata a rika yiwa Malaman jami’o’I gwajin magunguna ba dalibai kawai ba.
Wallafawa ranar:
Shugaban ya yi wannan kira ne a yayin da yake jawabi ga majalisar jami’ar a ranar juma’a da ta gabata.
Malam Abdul’aziz ya kara da cewa bai kamata a rika tilastawa dalibai gudanar da gwajin kwayoyi ba tare da su a suna yi ba, ba tare da suma suna yi ba, domin su kan su basu a wane matsayi suke ba.
A cewar shugaban hakan zai kara tsaftace tsarin jami’o’in da kuma inganta lamura wanda zai bunkasa harkokin ilimi.
Malamin Ya kuma kara da cewa, “Mun tattauna da ma’aikatar ilimi ta tarayya, kuma suna shirin gabatar wa dukkanin jami’o’in kasar cewa kafin kowane dalibi ya kammala rajistar karatu a jami’o’in, ya zama wajibi a yi masa gwajin magunguna.” Domin sanin matsayinsa.
VC din ya yi nuni da cewa, mafi kankantar nasarorin da aka samu a fannonin ci gaban ababen more rayuwa, ci gaban ilimi da kuma hidimar al’umma a lokacin mulkinsa ba zai yiwu ba sai da goyon bayan masu ruwa da tsaki a tsarin, don haka ya ci gaba da cewa wannan tsarin ma sai an hada karfi da karfe kafin a cimma nasara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu