Isa ga babban shafi
RAHOTO

Rashin lantarki ya haddasa karancin ruwa a arewacin Najeriya

Tsadar man fetur da hasken lantarki ya haddasa kamfar ruwa, musamman a arewa maso gabashin Najeriya, abin da ya jefa jama'a cikin mummunan yanayi.

Wasu mata kenan da ke neman ruwa a rijiyar burtsatse a gabashin kasar Ghana.
Wasu mata kenan da ke neman ruwa a rijiyar burtsatse a gabashin kasar Ghana. © Solidaridad
Talla

Mazauna jihar Adamawa na cigaba da ɗan ɗana kuɗarsu saboda rashin wadataccen ruwa, inda suka dora alhakin wannan matsala kan mahukuntan kasar.

Wannan matsala iyaye mata da dama sun ce na kokarin hana yaransu zuwa makaranta, kasancewar sai da ruwa za su girka abincin da za su ciyar da su, domin samun kuzarin shiga aji.

Sai dai masu sana'ar sayar da ruwan, sun ce rashin lantarki da kuma tsadar man fetur ne ya haifar musu da wannan matsala, domin sai sun yi da kyar suke samun ruwan da za su sayar.

shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken rahoton Ahmad Alhassan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.