Isa ga babban shafi
Kasuwanci

Yadda rufe iyakar Benin ya haifar da tsadar rayuwa a Nijar

Wallafawa ranar:

Shirin "Kasuwa akai Miki dole" na wanan mako tare da Ahmed Abba ya leka ne jihar Dosso dake Jamhuriya Nijar, yankin da ke kan iyaka da birnin Cotonou na Jamhuriya Benin inda jama'a suka shiga matsanancin halin tsadar rayuwa tare da kariyar tattalin arziki, sakamakon takun-kuman da Kungiyayoyi irinsu ECOWAS ko CEDEAO suka laftawa kasar, saboda Juyin mulkin da Sojoji sukayi.

Manyan motoci yayin da suka yi jerin gwano akan iyakar Najeriya da Nijar.
Manyan motoci yayin da suka yi jerin gwano akan iyakar Najeriya da Nijar. © Daily Trust
Talla

A Ranar 9 ga Watan Octoba da ya wuce Jamhuriya Benin ta rufe iyakar dake tsakaninta da makwabciyarta Jamhuriyar Nijar, bayan matakin da Kungiya ECOWAS ko CEDEAO ta dauka bayan da sojoji suka karbe mulki Ranar 26 ga watan Yuli wajen hambarar da shugaban Mohamed Bazoum.

Jamhuriyar Bénin ta dauki matakin soke duk wata hulda cinikaya da gwamnatin sojin Nijar.

Wanan matakin dai ya janyo hauhawa farashin Kayan bukatun jama'a na yau da kullun tare da haifar da koma bayan tattalin arziki a wasu sassan kasar, masamman  yankin Dosso, jiha daya tilo a Nijar da ta yi iyaka da Bénin har tsawan kilimita 150 daga yammacin Kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.