Isa ga babban shafi

Rasha ta soki kasashen Yamma kan shirin watsi da makamashin mai da iskar gas

Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ya zargi kasashen yammacin duniya da hargiza kasuwannin mai da iskar gas ta duniya, ta hanyar gaggauta sauya sheka zuwa makamashin mara gurbata muhalli tare da matsin lamba ga sauran kasashe da su yi hakan.

Shugaban Rasha Vladimir Putin.
Shugaban Rasha Vladimir Putin. AP - Sergey Guneyev
Talla

Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ya ce kasashen yammacin duniya da ba su da arzikin mai ko iskar Gas, don haka suke daukar matakan zango kasa ga tattalin arzikin kasashen ciki harda kasarsa.

"A hakikanin gaskiya, dalilan da ke haifar da munanan al'amura a bangaren makamashi su ne ayyukan da kasashen yammacin duniya ke yi na rashin sanin ya kamata, wajen yanke shawarar sauya fasalin makamashi, tare da tilastawa kasashe kaurewa man fetir da Iskar gas, ahali kuwa wasu kasashen ba su shirya ba ta fuskar karfin tattalin arziki, saboda basu da wasu hanyoyin dogaro”

Ya ce kauracewa makamashin Rasha da kasashen yamma suka yi a matsayin martani kan mamayar da ta yi wa Ukraine ya haifar da babbar illa ga tsaron makamashi a duniya.

Lavrov ya ce dakatar da bututun iskar gas na Nord Stream daga Rasha zuwa Turai a bara ya hana nahiyar samun iskar iskar gas mai arha, tare da dogaro da hajar mai tsada daga Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.