Isa ga babban shafi
Turkiya

Turkiya ce za ta daidaita jirgin Concordia – Italiya

Hukumar kula da ayyukan cikin gidan kasar Italiya, ta ce mai yiwuwa a baiwa kasar Turkiya kwantirakin daidaita jirgin Costa Concordia da ya yi hadara a shekarar 2012.

Jirgin Costa Concordia na kasar Italiya da ya yi hadari a shekarar 2012
Jirgin Costa Concordia na kasar Italiya da ya yi hadari a shekarar 2012 REUTERS/Tony Gentile
Talla

A watan Mayun wannan shekarar ake sa ran kasar ta Italiya za ta yanke hukuncin kasar da za ta bawa kwantirakin, amma bayanan dake fitowa daga kasar ta Italiya na nuna cewa ga dukkan alamu kasar Turkiya za a baiwa.

Sauran kasashen dake neman kwantirakin akwai Faransa da Birtaniya da kuma Norway.

A farkon shekarar 2012 jirgin ruwan Costa Concordia ya tintsire a kasar ta Italiya, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 32.

Rahotanni sun ce yanzu ana shirin farfasa jirgin bayan da aka daga shi a watanni baya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.